Ban aikata ko daya daga cikin tuhumar da ake mani ba - Zaura

Ban aikata ko daya daga cikin tuhumar da ake mani ba - Zaura

Yayinda hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da dan takarar gwamna a jam’iyyar Green Party of Nigeria (GPN) Abdulsalam Abdulkareem Zaura da wasu a gaban Alkali Lewis Allagoa da ke babbar kotun tarayya, Kano kan tuhume-tuhume tara na zambar kudi $1,320,000, dan takarar gwamnan yace lallai an shirya shari’an ne domin lalata siyasarsa.

Zaura ya karyata karban kudi daga hannun kowa, inda ya kara da cewa ya rigada ya karyata hakan ga EFCC da kuma jihar cewa bai aikata ko daya daga cikin tuhumar da ake masa ba a kotu.

Ya kuma bayyana cewa lamarin na a kotu kuma kotu ce kadai za ta bayyana gaskiya.

Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa lamarin tsantsar siyasa ce, majiyar ta kara da cewa kokari ake na durkusar da kudirin siyasar dan takarar gwamnan na GPN.

Ban aikata ko daya daga cikin tuhumar da ake mani ba - Zaura
Ban aikata ko daya daga cikin tuhumar da ake mani ba - Zaura
Asali: Depositphotos

“Muna kallon wannan a matsayin wani makirci na siysa, amma muna sanya ran cewa Alhaji Zaura ne zai yi nasara a kotu,” cewar majiyar.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta damfari dan majalisar wakilai N15m

A halin da ake ciki, an dage sahri’an zuwa ranar 29 da kuma 30 ga watan Janairun, 2019 don ci gaba da sauraron karar.

A wani lamari na daban, mun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) a jiya Alhamis, 22 ga watan Nuwamba ta yi bayanin cewa kariyar da kundin tsarin mulki ta bayar shine dalilin da yasa ba za su iya yin wani yunkuri ba akan Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano wanda a yanzu ake zargi da karban cin hancin miliyoyin daloli.

Wannan sharhin na zuwa ne bayan shugaban EFCC, Ibrahim Magu ya ki amsa tambaya game da Ganduje a wani taron manema labarai da aka yi kwanan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng