Za mu sadaukar da rayuwar mu don al’umman mu – Yan bangan Zamfara

Za mu sadaukar da rayuwar mu don al’umman mu – Yan bangan Zamfara

Sabbin mambobin yan tsaron sa kai wato Joint Task Force (CJTF) a Zamfara sun bayyana cewa za su sadaukar da rayuwar su domin kare al’umman su duk da hatsarin da ke tattare da yin hakan.

Wasu sabbin mambobin kungiyar da aka kwasa kwanan nan, wanda suka yi Magana don nuna jajircewarsu sun bayyana cewa a shirye suke da su kare garurwansu domin fitar da jihar daga matsalar yan fashi da makami.

Sun bayyana cewa suna sane da hatsarin da ke tattare da hakan amma a shirye suke don fuskantar kalubalen.

Za mu sadaukar da rayuwar mu don al’umman mu – Yan bangan Zamfara
Za mu sadaukar da rayuwar mu don al’umman mu – Yan bangan Zamfara
Asali: Depositphotos

“Za mu sanya rayuwar mu a kan hanya domin kare jihar mu. Ba za mu gaji a kudirinmu ban a don ganin mun fatattaki yan iskan da ke kaiwa kauyukan mu hare-hare ba,” cewar wani Musa Kabir.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta damfari dan majalisar wakilai N15m

Yace sun yanke shawarar kare mutanensu domin yin maganin yan fashi da makami da kuma barayn dabbobi da suka addabi jihar tsawon shekaru da dama ba tare da an dauki wani kwakwaran mataki ba akansu.

Wani dan kungiyar daga karamar hukumar Zurmi yace ba don sun shiga lamarin ba da a yanzu yan daba sun shafe kauyukan Zamfara da dama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng