Wata mata ta damfari dan majalisar wakilai N15m

Wata mata ta damfari dan majalisar wakilai N15m

An gurfanar da wata mata mai shekara 37, Amarachukwu Chineke, wacce aka zarga da damfarar dan majalisar wakilai, mai wakiltan mazabar Idah da ke jihar Kogi, Emmanuel Egwu, $49,800, a gaban kotun majistare da ke Igbosere, a jihar Lagas.

Chineke wacce ba’a bayyana adireshin gidanta ba na fuskantar tuhuma na karya, yaudara da kuma sata.

Dan sanda mai kara, Sergeant Friday Mameh ya fada ma kotu cewa wacce ake kara da wasu sun aikata laifin a ranar 19 ga watan Satumba a unguwar Abraham Adesanya, Lekki Lagas.

Yayi ikirarin cewa Chineke ta samu kudin a karkashin karya da yaudarar cewa tana a matsayin chanja kudin wanda yayi daidai da N15,438,000.

Wata mata ta damfari dan majalisar wakilai N15m
Wata mata ta damfari dan majalisar wakilai N15m
Asali: Getty Images

Mameh ya bayyana cewa wacce ake karar ta hada kai da wasu da ba’a gano ba har yanzu wajen satar $49,800, dukiyar Emmanuel Egwu, bisa yaudarar cewa za su bashi naira daidai da kudin.

Sai dai wacce ake zargin ta ki amsa tuhumar da ake mata.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta ci tarar dan majalisa N120,000 kan amsar cin hancin N4.5m

Don haka, mai shari’a ta kotun majistare, Folashade Botoku ta bayar da belinta, kan naira miliyan 2 da wadanda za su tsaya mata mutun biyu.

An dage sauraron shari’an zuwa ranar 10 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng