Kashin Boko Haram ya bushe: Jiragen yaki na musamman da shugaba Buhari ya sayo sun iso

Kashin Boko Haram ya bushe: Jiragen yaki na musamman da shugaba Buhari ya sayo sun iso

Da safiyar yau, Alhamis, ne jiragen yaki na musamman da shugaba Buhari ya sayo tun 2016 daga kasar Amurka su ka iso Najeriya.

Yazu haka Najeriya ce kasa uku, bayan kasarBrazil da Saudiyya, da kasar Amurka ta yarda ta sayarwa da irin wadannan jirgin sama na yaki da za a iya kai hari da su da daddare tare da dauko hotuna daga nesa.

An bayyana cewar rashin cika wasu ka'idojin Amurka, a kan amfani da jiragen, da Najeriya ta yi ne ya kawo jinkirin sakar ma ta da jirage tuntuni.

Ana sa ran zuwan jiragen zai taimaka a yakin da jami'an sojin Najeriya ke yi da 'yan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da kuma ma su garkuwa da mutane.

Kashin Boko Haram ya bushe: Jiragen yaki na musamman da shugaba Buhari ya sayo sun iso
Jiragen yaki na musamman da shugaba Buhari ya sayo sun iso
Asali: Facebook

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar hukumar 'yan sanda a jihar Bauchi ta bayyana cewar rikicin da ya barke ranar Lahadi a unguwar Yelwa da ke garin Bauchi, ba shi da alaka da addini ko kabilanci.

Hukumar ta ce sabani ne tsakanin wasu kungiyoyin matasa biyu da ta rikide zuwa rikici.

DUBA WANNAN: Tone-tone: Jonathan ya bayyana gwamnonin da su ka ci amanarsa a 2015

Wannan bayanai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun DSP Kamal Datti Abubakar, kakakin rundunar, da hukumar ta fitar a yau, Laraba.

Sanarwar ta kara da cewar, hukumar 'yan sanda na wannan bayanai ne a matsayin raddi ga labaran da ke yawo a kafar sada zumunta da ke nuna cewar rikicin na da alaka da addini ko kabilanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng