Magu ya nemi a dena kai shari'ar EFCC gaban wata alkaliya

Magu ya nemi a dena kai shari'ar EFCC gaban wata alkaliya

- Hukumar EFCC ta nemi Babban Alkalin Najeriya, Walter Onnoghen ya hana mai shari'a Binta Nyako sauraron duk wata shari'a mai alaka da hukumar

- EFCC ta bukaci hakan ne domin a halin yanzu hukumar ta gurfanar da tsohon gwamna Adamawa, Murtala Nyako wanda shine mijin Binta Nyako

- Hukumar tana fargabar akwai yiwuwa mai shari'a Binta Nyako za ta iya kawo cikas a shari'ar saboda kasancewar mijinta ake tuhuma

Magu ya nemi gaban wata alkaliya
Magu ya nemi gaban wata alkaliya
Asali: Depositphotos

Shugaban rikon kwarya na hukumar yaki da rashawa, (EFCC), Mr Ibrahim Magu ya rubuta wasika da Babban Alkalin Najeriya, Justice Walter Onnoghen inda ya ke nema a hana mai Shari'a Binta Nyako sauraron duk wani shari'a da ya shafi hukumar.

EFCC ta bayyana cewa akwai yiwuwar mai Sharia Nyako za ta iya kawo cikas ga gudanar da shari'ar saboda a halin yanzu hukumar ta gurfanar da mijinta wato tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako a kotun inji mai magana da yawun hukumar, Mr Tony Orilade.

DUBA WANNAN: Almundahar N27bn: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Abia

A baya, lauyan EFCC, Onjefu Obe ya shaidawa kotun a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018 yayin gudanar da shari'ar wasu mutane hudu da ake zargi da satar man fetur cewa EFCC za tafi samun kwanciyan hankali idan aka karbe shari'an daga hannun Justice Nyako saboda akwai yiwuwar za ta saka son zuciya a cikin shari'ar.

Ana tuhumar Umar Audu Bida, Truth Igogori, Ifenyinwa Nwankwesiri da Ogechukwu Obaji da laifin yunkurin karkatar da man fetur wanda kudinsa ya kai $1 miliyan.

Anyi ikirarin sun damfari Donald Latella na North Park LLC ne inda suka ce za su samar masa da man fetur samfurin Bonny Light amma hakan bai yiwu ba.

Dukkansu sun musanta zargin da ake musu yayin da kotu ta karanto musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: