Bikin mauludi: Babban Sarki a arewa ya nemi jama'a su goyawa Buhari baya

Bikin mauludi: Babban Sarki a arewa ya nemi jama'a su goyawa Buhari baya

- Alhaji Faruk Umar Faruk, sarkin Daura, ya bukaci 'yan Najeriya da su cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari domin ta samu nasarar gyara tattalin arzikin kasa

- Sarkin ya bayyana cewar gwamnatin shugaba Buhari ta shimfida titunan mota a kauyuka da birane da kuma layin jirgin kasa

- Sarkin na Daura ya yi amfani da bikin Sallar-Gani wajen nada Alhaji Yakubu Gobir a matsayin sabon wazirin kasar Hausa, sarauta mai daraja ta biyu a kasar Hausa

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, ya bukaci 'yan Najeriya da su cigaba da goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari domin ta samu nasarar gyara tattalin arzikin kasa.

Alhaji Faruk ya yi wannan kira ne a garin Daura yayin bikin murnar Sallar-Gani mai dumbin tarihi.

Sarkin ya bayyana cewar gwamnatin shugaba Buhari ta shimfida titunan mota a kauyuka da birane da kuma layin jirgin kasa.

Kazalika ya yi kira ga shugaba Buhari da ya cigaba da jajircewa wajen yiwa kasa aiyukan da za su inganta rayuwar jama'a da tattalin arzikin kasa.

Bikin mauludi: Babban Sarki a arewa ya nemi jama'a su goyawa Buhari baya
Buhari da sarkin Daura
Asali: Facebook

Sarkin na Daura ya yi amfani da bikin Sallar-Gani wajen nada Alhaji Yakubu Gobir a matsayin sabon wazirin kasar Hausa, sarauta mai daraja ta biyu a kasar Hausa.

A cewar Alhaji Farouk, masarautar Daura ce ke da alhakin nada wazirin kasar Hausa saboda matsayin da masarautar ke da shi a tarihin yaren Hausa.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar a jiya, Laraba, ne gwamnonin yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo su ka ziyarci shugaba Buhari tare da yin wata ganawa ta sirri.

DUBA WANNAN: Kaddamar da littafin Jonathan: Kallo ya koma kan Atiku

Sai dai bayan kammala ganawar ta su, shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso gabas, Mista Dave Umahi, gwamnan jihar Ebonyi, ya ce sun ziyarci shugaban kasar ne domin yi ma sa godiya bisa fitar da kudin kwangilar gina gadar Neja ta biyu tare da rokonsa a kan a rage wa'adin kammala aikin gina gadar daga adadin wata 42 da 'yan kwangilar su ka bayar zuwa wata 24.

Umahi ya ce, "mun ziyarci fadar shugaban kasa ne domin yi ma sa godiya amadadin al'ummar yankin kudu maso gabas bisa bawa kamfanin Julius Berfer kwangilar sake gina gadar Neja a kan biliyan 206."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel