Yanzu Yanzu: Yan majalisar wakilai 2 sun sake barin APC
- Yan majalisar wakilai biyu sun sakesauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulki
- Wadanda suka sauya shekar sune Ahmed Abu daga Jihar Niger da kuma Stephen Olemija daga Jihar Ondo
- Sun koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da kuma jam’iyyar Action Alliance
Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyu a majalisar wakilai sun sanar da ficewarsu daga jam’iyyar mai mulki.
Idan za ku tuna a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba ma wasu mambobi biyu suka bar APC.

Asali: Twitter
A zaman majalisar na yau Alhamis, 22 ga watan Nuwamba, kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya karanta wasiku daga Ahmed Abu (Jihar Niger) da kuma Stephen Olemija (Jihar Ondo).
KU KARANTA KUMA: 2019: Masoya sun kawo karshen addu’o’in kwanaki 40 da suka yi wa Buhari (hotuna)
Sun kuma bayyana komawarsu jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da kuma jam’iyyar Action Alliance.
A wani lamari na daban, mun ji cewa Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kokari don ganin ta kawo jihohi 30 a zaben 2019.
Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba lokacin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya kaddamar da kwamitocin sulhu domin magance matsalar zaben fidda gwani da ya addabi jam’iyyar a fadin kasar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng