2019: APC na hararar jihohi 30 na kasar - Shettima

2019: APC na hararar jihohi 30 na kasar - Shettima

- Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana cewa jam’iyyar APC zat ta lashe jihohi 30 a zaben 2019

- Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba lokacin kaddamar da kwamitocin sulhu domin magance matsalar zaben fidda gwani da ya addabi jam’iyyar a fadin kasar

- Shettima yayi alkawarin cewa kwamitocin ba za su ba jam’iyyar kunya ba

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kokari don ganin ta kawo jihohi 30 a zaben 2019.

Ya bayyana hakan a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba lokacin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya kaddamar da kwamitocin sulhu domin magance matsalar zaben fidda gwani da ya addabi jam’iyyar a fadin kasar.

2019: APC na hararar jihohi 30 na kasar - Shettima
2019: APC na hararar jihohi 30 na kasar - Shettima
Asali: Depositphotos

Shettima wanda ya ce neman kujerar mulki ba taron shan shayi bane, yace yadda aka dauki lamarin na da matukar muhimmanci.

KU KARANTA KUMA: Zambar $3m: Lawan ya nemi cin hanci daga gare ni – Femi Otedola

Yace akwai bukatar jam’iyyar ta dauki matakin sasanta gidanta sannan yayi alkawarin cewa kwamitocin ba za su ba jam’iyyar kunya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel