Rayyuka da yawa sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya faru a Yobe

Rayyuka da yawa sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya faru a Yobe

- Anyi wani mummunan hatsarin mota a hanyar Damaturu zuwa Potiskum a jihar Yobe

- Mutane bakwai sun rasa rayyukansu sannan wasu mutane goma sun samu raunuka daban-daban

- Hukumar kiyaye haddura na kasa FRSC ta bayyana cewa gudu fiye da kima da amfani da taya mara kyau ne ya janyo hatsarin

Rayyuka da yawa sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya faru a Yobe
Rayyuka da yawa sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya faru a Yobe
Asali: Twitter

Mutane bakwai sun riga mu gidan gaskiya sannan wasu 10 sun jikkata a wani hatsarin mota da ya afku yayin da wata bas mai dauke da fasinjoji 18 zuwa jihar Gombe tayi hatsari a hanyar Damaturu zuwa Potiskum a jihar Yobe.

A yayin da ya ke tabbatar da hatsarin, Secta Kwamanda na hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) na jihar, Muhammad Sani Hamzat ya ce fasinjoji 17 be cikin motar bas din.

Ya bayyana cewa direban yana gudu ne lokacin da tayan baya na motar ya fashe hakan ya sanya motar tayi kundunbala zuwa dayen bangaren titin kuma ta kife.

DUBA WANNAN: Almundahar N27bn: EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan Abia

Ya ce mutane bakwai sun mutu a nan take sannan jami'an hukumar sun ceto wasu mutane 10 da suka samu raunukka daban-daban.

"Wadanda suka samu raunukkan suna karbar magani a asibiti yayin da gawawakin wadanda suka rasu suna ajiye a dakin ajiye gawawaki na asibitin," inji shi.

Ya ce gudun da ya wuce kima da kuma amfani da tayoyin da suka lalace ne ya janyo hatsarin.

A wani rahoton, Legit.ng kawo muku cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Trrust, Mr Gbenga Olawepo-Hashim ya yi alkawarin zai biya N50,000 albashi mafi karanci a cikin watanni shida na farko idan aka zabe shi shugaban kasa.

Olawepo Hashin ya furta hakan ne a yayin kaddamar da yakin neman zabensa a babban birnin tarayya, Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164