Jonathan ya fara shan suka da raddi bayan kaddamar da littafinsa

Jonathan ya fara shan suka da raddi bayan kaddamar da littafinsa

A jiya, Talata, ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar da wani littafi mai taken "my transition hours" da ya rubuta. An kaddamar da littafin ne a Transcorp Hilton da ke Abuja.

Jonathan ya yi tsokaci a kan batutuwa ma su dama a cikin littafin, musamman a kan yadda ya fadi zaben shekarar 2015 da kuma abubuwan da su ka faru kafin da kuma bayan zaben.

A wani bangare na littafin, Jonathan ya zargi kungiyar dattijan Arewa (ACF) da kuma wasu kungiyoyin yankin da taka muhimmiyar rawa a kayar da shi zabe.

Kazalika ya lissafa wasu mutane da ya ce sun ba shi shawara kan cewar kar ya mika mulki bayan an sanar da sakamakon zabe.

Jonathan ya fara shan suka da raddi bayan kaddamar da littafinsa
Jonathan
Asali: Twitter

Sai dai a nata bangaren, ACF ta yi watsi da batun cewar ta taka rawa a kayar da Jonathan tare da yi ma sa radadin cewar shine ya kayar da kansa, a saboda haka ya daina neman wanda zai dorawa laifi.

DUBA WANNAN: Faifan bidiyo: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci a kan tuhumar Ganduje

A yayin da ACF ke wannan raddi, wasu ma'abota amfani da dandalin sada zumunta na Tuwita sun nemi mutanen da Jonathan ya ce sun bashi shawara kar ya mika mulki da su bayyana dalilinsu na bashi wannan shawara.

Daga cikin mutanen akwai Osita Chidoka, Ngozi Okonjo Iweala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel