2019: Za mu zuba idanu sosai akan kamfen din jam’iyyun siyasa - INEC

2019: Za mu zuba idanu sosai akan kamfen din jam’iyyun siyasa - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa za ta zuba idanu sosai akan kamfen din jam’iyyun siyasa domin tabbatar da cewa ba su taka doka da sharudan da aka gindaya ba.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba a wajen taron kwamishinonin zabe wanda aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa hukumar ta jajirce wajen kula da kamfen din yan takara domin ganin ba su shillake ka’ida da doka ba.

2019: Za mu zuba idanu sosai akan kamfen din jam’iyyun siyasa - INEC
2019: Za mu zuba idanu sosai akan kamfen din jam’iyyun siyasa - INEC
Asali: Depositphotos

Mahmood ya bayyana cewa taron baya da suka gudanar tare da kwamishinonin zabe a watanni biyu da suka gabata ya mayar da hankali ne wajen shirye-shiryen zaben 2019, musamman kan ci gaba da rijistan masu zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya nada Musa Abaji a matsayin sabon alkalin kotun koli R

Ya kuma jadadda cewa hukumar na aiki don ganin ta gama da rijista domin shine tushen zabe na gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng