An yankewa wani Barawon Keken 'Dinki hukuncin dauri na watanni 14 a jihar Sakkwato

An yankewa wani Barawon Keken 'Dinki hukuncin dauri na watanni 14 a jihar Sakkwato

A yau Laraba wata babbar kotun majistire da ke can Birnin Shehu, ta zartar da hukuncin dauri na tsawon watanni 14 ga wani Matashi dan shekara 21, Bello Labaran, bisa aikata laifin dan hali na satar wani Keke Dinki da darajarsa ta kai N50, 000.

Bisa tsari daban-daban na zartar da hukunci, Mai gudanar da shari'ar, Mallam Nuraddeen Bello, bai bayar da zabin biyan tara ba ga wannan Matashin da son banza ya janyo ma sa salolan tsiya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta ruwaito, Kotun bayan kammala bincikenta ta kama wannan Matashi dumumu da wannan laifi da ake tuhumarsa, inda gogan naka wanda mazaunin unguwar Aduworuwa ne ya amsa laifinsa ba tare da wata-wata ba.

An yankewa wani Barawon Keken 'Dinki hukuncin dauri na watanni 14 a jihar Sakkwato
An yankewa wani Barawon Keken 'Dinki hukuncin dauri na watanni 14 a jihar Sakkwato
Asali: Twitter

Jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, Labaran tare da wani abokinsa na kulla wannan tuggu, Babangida Tuwo wanda a halin yanzu ya bazama, sun yi tarayya wajen ketare iyakar wani gida mallakin Muhammad Sama'ila da ke unguwar Bazza, inda suka yi awon gaba da wani keke dinki da darajararsa ta kai N50, 000.

KARANTA KUMA: Gwamnatin shugaba Buhari ta tsananta rashawa a Najeriya

A yayin da hukumar 'yan sanda reshen cibiyarta na Dadin Kowa tayi kacibus da wannan korafi a ranar 18 ga watan Satumban da ya gabata, jaridar Legit.ng ta fahimci cewa wannan mummunan laifi na cin karo da sashe na 97, 356 da kuma sashe na 288 cikin dokokin kasa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata babbar kotun Majistire da ke garin Ilorin na jihar Kwara, ta bayar da umarnin garkame wani mutum, Afolabi Stephen mai shekaru 42 a duniya, bisa aikata laifin sojan gona da wani babban mukami na dakarun sojin kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng