Wasu maza 2 da suka yiwa wata mace ta'asa da adda sun gamu da fushin kotu

Wasu maza 2 da suka yiwa wata mace ta'asa da adda sun gamu da fushin kotu

A yau Laraba 21 ga watan Nuwamba ne 'yan sanda suka gurfanar da wasu mutane biyu a kotu da ke zamnata a Karu a Abuja bisa zarginsu da sarar wata Vera Atule kafa da adda a kafafuwanta.

Ana tuhumar Abubakar Hassan mai shekaru 22 dda Abdulrazak Sani mai shekaru 22 da laifuka guda hudu wanda suka hada da hadin baki, sata da yiwa wani rauni sai dai matasan biyu sun musanta aikata laifin.

Dan sanda mai shigar da kara, Vincent Osuji ya shaidawa kotu cewa wanda ta shigar da karar, Atule da ke zaune a Anguwan Tiv, Karu Abuja ta shigar da kara a ofishin yan sanda ne a ranar 21 ga watan Octoba misalin karfe 11 na dare.

An gurfanar da maza biyu a kotu saboda sarar wata mace da adda
An gurfanar da maza biyu a kotu saboda sarar wata mace da adda
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

"Mai shigar da karar tayi ikirarin cewa a tana zaune a kofar gidanta da ke adreshin da aka ambata a sama ne wadanda ake zargin suka hada baki suka shigo gidanta dauke da sanduna da adda.

"Wanda ake kara sun yiwa Atule rauni a kafafunta biyu kafin daga bisani aka garzaya da ita asibiti inda ta kashe N6,500 wajen magani.

"Mai shigar da karar kuma tayi ikirarin cewa wanda ake tuhuma sun sace mata wayar salula da kudinsa ya kai N11,500," inji Osuji.

Ya ce laifukan da suka aikata ya ci karo da sashi na 80, 269, 250 da 287 na Penal Code.

Alkalin kotun, mai shari'a Sani Mohammed ya bayar da belin wadanda ake zargin a kan N50,000 kowannensu tare da mutum daya da zai tsaya musu sannan ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Nuwamban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164