Yadda muka kakaba ma shugaban kasa Obasanjo takunkumi – Inji tsohon Gwamna Osoba
Tsohon gwamnan jahar Ogun, Olusegun Osoba ya bayyana yadda shi da sauran takwarorinsa tsofaffin gwamnoni suka kakaba ma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo takunkumi, suka hanashi rawar gaban hantsi a zamanin mulkinsa.
Osoba ya bayyana haka ne a yayin bikin kaddamar da littafi tarihin rayuwar tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom Obong Victor Attah da aka yi a ranar Talata 20 ga watan Nuwamba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace gwamnonin zamaninsa sun fi na yanzu hadin kai da karfi.
KU KARANTA: Barayi sun yi awon gaba da yaro dan shekara 7, sun kwakwule masa idanuwa a wata jahar Arewa
Osoba yace gwamnonin zamaninsa sun tsaya tsayin daka tare da mara ma takwarorinsu na jihohin kudu maso kudu baya don ganin gwamnatin Obasanjo ta sakan musu mara akan batun karin adadin kudin da gwamnatin tarayya ke basu daga kudin man fetir.
“Abin mamaki shine idan gwamnonin jam’iyyun adawa kamarmu da muka fito daga jam’iyyar AD, tare da Lam Adesina, muka yi magana, sai kaga Attah daga jam’iyyar PDP ya ara ya yafa, kai wani zubinma sai kaga yafi mai kowa shafawa, da haka ne muka yi maganin Obasanjo.
“Saboda muna sane cewa Abdulsalam Abubakar ya bar makudan kudaden da gwamnati zata raba ma gwamnoni, amma da zuwan Obasanjo sai ya kwashe kudaden ya saya ma kananan hukumomi motoci, haka yayi ta yi ma dokokin kashe kudin gwamnati karan tsaye, mu kuma muka garzaya kotu a karkashin jagorancin Attah, da haka muka samu nasara." Inji shi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari daya samu wakilin ministan tsare tsare da kasafin kudi, Udoma Udo Udoma ya yaba ma tsohon gwamnan, wanda ya bayyana shi a matsayin jagora nagari kuma uba a gareshi, inda yace shine shugaban sanatocin jahar Akwa Ibom a zamaninsa.
Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Odigie Oyegun, gwamnan jahar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, Ministan kwadago, Chris Ngige, tsohon gwamnan jahar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim.
Sauran sin hada da tsohon gwamnan jahar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole, yan majalisu na da dana yanzu, kwamishinoni na da na yanzu da sauran manyan mutane.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng