Kada ku mika kasar da damokradiyya ga barayi da yan iska – Obasanjo ya gargadi yan Najeriya

Kada ku mika kasar da damokradiyya ga barayi da yan iska – Obasanjo ya gargadi yan Najeriya

- Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bukaci yan Najeriya da su tabbatar da cewa ba su muka kasar da damokradiyya ga wadanda ya kira da suna barayi da yan iska ba

- Ya yi gargadin ne a lokacin da ya shugabanci taron kaddamar da littafin Goodluck Jonathan, ‘My Transition Hours,’ a Abuja a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba

- Obasanjo ya ce idan aka mika damokradiyar kasar ga mutanen da suka fada a wannan rukuni, za su iya amfani da hakan a matsayin makamin yakar mutane

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo wanda ya shugabanci taron kaddamar da littafin Goodluck Jonathan, ‘My Transition Hours,’ a Abuja a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba ya bukaci yan Najeriya da su tabbatar da cewa ba su muka kasar da damokradiyya ga wadanda ya kira da suna barayi da yan iska ba.

Legit.ng ta tattaro cewa Obasanjo ya ce idan aka mika damokradiyar kasar ga mutanen da suka fada a wannan rukuni, za su iya amfani da hakan a matsayin makamin yakar mutane.

Kada ku mika kasar da damokradiyya ga barayi, da yan iska – Obasanjo ya gargadi yan Najeriya
Kada ku mika kasar da damokradiyya ga barayi, da yan iska – Obasanjo ya gargadi yan Najeriya
Asali: UGC

Obasanjo ya tuna cewa a wani jawabi da wani dan damokradiya yayi ya ce ya fi son zama a Najeriya saboda idan abubuwa suka durkushe da safe, toh abubuwa za su lafa zuwa yamma.

“Don haka mu ci gaba da lafar da Najeriya,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Kada ku ba Buhari damar yin tazarce – Udeogaranya ga yan Najeriya

Obasanjo ya taya Jonathan murnar tafiyar da ritayarsa cikin kwanciyar hankali, inda ya kara da cewa wannan rayuwa da tsohon shugaban kasar ke gudanarwa ta jin dadi shine abunda kowa ke buri, inda ya bayyana hakan a matsayin ci gaba mai kyau.

Yace tsohon shugaban kasar na da wani hakki da ya rataya a wuyansa na ci gaba da yiwa al’umma da Ubangiji hidima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng