Magidanci ya dauki tsatstsauran mataki akan kwarton daya kama da matarsa a jahar Neja

Magidanci ya dauki tsatstsauran mataki akan kwarton daya kama da matarsa a jahar Neja

Rundunar Yansandan jahar Neja ta kama wani Magidanci mai suna Joseph Atanda mai shekau 40 da laifin kashe wani mutumi mai suna Umaru Yakubu a kauyen Kwagana dake cikin karamar hukumar Paikoro ta jahar Neja.

Majiyar Legit.com rundunar ta tabbatar da kama Atanda ne a ranar Talata, inda tace wasu jami’anta dake ofishin Yansandn Kanfin-koro ne suka samu nasarar cafkeshi bayan sun labarin kisan da ake zarginsa da aikatawa.

KU KARANTA: Gyaran ilimi: Gwamna Masari zai sama matasa 2000 aikin koyarwa a Katsina

Sai dai Abanda, wanda dan asalin kauyen Beni dake karamar hukumar Muya ya bayyana dalilinsa na kashe Umaru, inda yace ya kasheshi ne saboda ya kamashi yana saduwa da matarsa, kamar ya bayyana ma manema labaru.

Abanda ya kara da cewa ya dade yana jan kunnen Umaru ya fita daga harkar matarsa, ma’ana ya daina bibiyan matarsa amma ya ki ji, daga nan sai ya yanke shawarar daukan mataki idan har Umaru bai nesanta kansa daga matarsa ba, kwatsam sai ga shi ya kamasu a cikin daji suna saduwa.

Ganin ya kamasu turmi da tabarya ne ya harzuka Atanda, wanda nan take ba tare da bata lokaci ba ya samu wani icce ya dinga dukan Umaru da shi har sai da yaga baya motsi, ya tabbatar ya mutu, kuma yace baya nadama, a shirye yake ya dauki duk hukuncin da aka daukan masa.

“Na sha gargadinsa ya daina bibiyan matata, na ja kunnensa ya daina kwanciya da matata don idan ba haka b azan kashe shi, kuma na shirya daukan duk hukuncin da zai biyo baya idan na kasheshi, karshe dai shine a kaini gidan yari, ba matsala.

“Na kashe shi ne saboda girman zunubin daya aikata ma iyalina, wannan laifin da yayi babban laifi ne a Musulunci, haramun ne wani ya kwanta da matar wani a addinin Musulunci, laifi ne dake dauke da hukuncin kisa.” Inji shi.

Daga karshe Kaakakin rundunat Yansandan jahar ya bayyana cewa sun kaddamar da binciken kwakwaf don tabbatar da gaskiyar lamarin, daga karshe kuma zasu gurfanar da Atanda gaban Kotu don yanke masa hukuncin daya dace da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: