2019: Kada a ji komai za mu kawo wa APC Sokoto - Wamakko

2019: Kada a ji komai za mu kawo wa APC Sokoto - Wamakko

Shugaban kungiyar sanatocin arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi hasashen cewa cikin rowan sanyi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta lashe zabe a Sokoto, yayinda yake yaba ma tarin goyon bayan da jam’iyyar ke samu a dukkan matakai na kasar.

Sanata Wamakko, ya yi Magana ne a gidansa na Gawon Nama, da ke Sokoto lokacin da yake jawabi ga taron jiga-jigai da mambonbin jam’iyyar jim kadan bayan dawowarsa daga wani ziyarar aiki a Abuja.

Da yake Magana akan zaben 2019, Wamakko ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkanin yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), za su lashe zabe mai zuwa.

2019: Kada a ji koma za mu kawo wa APC Sokoto - Wamakko
2019: Kada a ji koma za mu kawo wa APC Sokoto - Wamakko
Source: Depositphotos

Wamakko ya kuma bayyana cewa jam’iyyar da yan takaranta a dukka matakai ba za su ba yan Najeriya kunya ba kuma za su cika alkawaransu.

Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyya da su guji duk wani tashin hankali da hayaniya a lokaci da bayan zabe.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: N30,000 bai yi yawa ba don haka ku biya – Sanata Ndume

A wani lamari na daban, tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdusalami Abubakar ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kawo zaman lafiya a kasar ta hanyar amsar sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 wanda ya sha kasa.

A cewarsa kasar Najeriya bata san irin godiyar da za ta yiwa Jonathan ba bisa wannan karamci da dattako da ya nuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng