Wani Mahaifi yayi lalata da ɗiyarsa 'yar shekara 2 a jihar Legas

Wani Mahaifi yayi lalata da ɗiyarsa 'yar shekara 2 a jihar Legas

Za ku ji cewa hukumar 'yan sanda ta cafke wani Mahaifi, Peter Adeda, bisa zarginsa da laifi aikata lalata da ɗiyarsa 'yar shekara 2 a unguwar Westwood dake hanyar Oyetola Olafisoye a jihar Legas.

Binciken kwararrun kiwon lafiya ya tabbatar da cewa, ko shakka ba bu an keta haddin wannan karamar yarinya inda yayin tuntubarta dangane da wanda ya yi mata wannan aika-aika ta yi nuni da Mahaifin ta tare da da zayyana yadda lamarin ya kasance.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, CSP Chike Oti, wanda ya bayar da tabbacin wannan lamari ya bayyana cewa, tuni kwamishinan 'yan sanda na jihar Edgal Imohimi, ya bayar da umarnin mika wannan lamari zuwa ga cibiyar kula da cin zarafi da keta haddi domin ci gaba da bincike.

Wani Mahaifi yayi lalata da ɗiyarsa 'yar shekara 2 a jihar Legas
Wani Mahaifi yayi lalata da ɗiyarsa 'yar shekara 2 a jihar Legas
Asali: Facebook

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan cibiya a halin yanzu na kuma gudanar da bincike kan wani dattijo dan shekara 58, Abdullahi Garuba, bisa zarginsa da laifin aikata luwadi da wasu kananan yara biyu a karamar hukumar Oshodi a ta jihar Legas.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai binciki hukuncin Gwamnoni kan mafi karancin Albashin Ma'aikata

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, asirin wannan dattijo ya tonu yayin da al'ummar gari suka nemi jin masaniyar alakarsa da kananan yaran biyu, inda bincike ba tare da wani zurfi ya tabbatar da wannan zargi.

Kazalika jaridar ta kuma ruwaito cewa, 'yan fashi da makami sun sake kai hari wani Banki a jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya inda rayukan mutane hudu suka salwanta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng