PDP ce ta fara kawo siyan kuri’a – Sanata Ndume
Sanata mai wakiltan yankin Borno ta Kudu, Ali Ndume ya zargi babbar jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da fara kawo siyan kuri’a a tsarin zaben Najeriya.
Ndume wanda ya bayyana hakan a Abuja yayinda yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) na martani ne akan zargin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na amfani da shirinta na tallafawa al’umma ciki harda TradeMoni don siyan kuri’u.
Dan majalisan ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasar jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani ne ta hanyar siyan kuri’a.

Asali: UGC
Ndume ya ce a bangaren dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki babu wanda aka biya ko sisin kwabo kafin Shugaban Kasa Muhammadu ya zamo dan takarar jam’iyyar.
Ya bayyana cewa shugaban kasar bai nemi kowa ya janye masa ba a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar balle har a kai ga siye wakilan jam’iyyar.
KU KARANTA KUMA: Shirin tsige Saraki na nan daram – Sanata Ndume
Ya kuma bayyana cewa kudi ba zai taba daina tasiri ba a siyasar kasa kamar Najeriya domin ana hakan ko a kasashen da suke cike damokradiyya irin su Amurka da sauransu.
Ya ce daya daga cikin dalilan da yasa tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya kayar da Hilary Clinton a zaben fidda gwani na jam’iyyar damokradiyya a 2008 ya kasance saboda ya fi ta kudi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng