Mai kudin China Jack Ma ya bar kamfaninsa na N15trn don ya zama malamin makaranta
A farkon watan Oktba 2018, wanda yayi daidai sa cikarsa shekara 54, mai kudin China, Jack Ma ya sanar da cewa zai sauka daga matsayin shugaban babban cibiyar cinikin nan na Alibaba.
Jack Ma shahararren dan kasuwar nan mammalakin babban kamfanin nan na China ba wai zai yi ritaya bane. Yana so ya sake zama malamin makaranta ne.
Da kudin da ya kai kimanin dala biliyan 40.5, Ma ya kasance daya daga cikin masu kudin duniya kuma ya kasance fitacce. Ya kasance mutun mai goggayya da shugabannin duniya.
Shawarar Ma na janyewa daga babban matsayi a Alibaba zai sabonta wasu lamura ga kamfanin na dala biliyan 420, wanda ya habbaka a yanar gizo daga gidansa zuwa babban kamfani a duniya.

Asali: UGC
Asalin Ma ya fito ne daga gidan talakawa sannan ya sha gwawarma a rayuwarsa har zuwa lokacin day a kammala karatunsa.
Bayan nan ya nemi aiki a wurare daban-daban amma sai su ki daukar sa aiki, inda daga nan ne ya koyi darasi na rayuwa.
KU KARANTA KUMA: Barazanar yan siyasa ba zai tsorata mu ba - INEC
Aikin koyarwa ya kasance aiki da ya yi a baya, har ya kai matakin Farfesa a harshen Turanci.
A cewarsa zai koma harkar koyarwa ne domin har yanzu da sauran jini a jikinsa kuma yana da mafarki da yake so ya cimma a rayuwa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng