Jam'iyyu 38 sun zabi Atiku a matsayin dan takarar su na shugaban kasa
Cibiyar bayar da shawarwari na jam'iyyun siyasa (IPAC) reshen jihar Adamawa wadda ta kunshi jam'iyyun siyasa 38 sun zabi dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar a matsayin dan takararsu a zaben 2109.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa IPAC ta cimma wannan matsayar ne a ranar Litinin 19 ga watan Nuwamba bayan ta zabi sabbin shugabanin ta a Jihar.
Rahoton ya ce sakataren yada labarai na IPAC, Usman Bakawu yana cewa kungiyar ta fara hada jan al'umma domin su goyi bayan Atiku Abubakar.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi
"A jiya, tsohon shugaban kasa ya karbi bakuncin mu kuma ya bamu shawarwari masu amfani kan yadda za mu hada kan al'umma domin cigaban jihar mu.
"Ina son kuma in tabbatar mu ku da cewa IPAC reshen jihar Adamawa tana tare da Atiku kuma zamu fara aiki domin hada kan jama'a domin zaben Wazirin Adamawa," inji shi.
Legit.ng ta gano cewa Tahir Shehu wanda shine Ciyaman din jam'iyyar PDP a jihar Adamawa shine aka zaba a matsayin jagoran IPAC na jihar.
An ruwaito cewar an fafata a wajen zaben amma daga karshe Ciyaman din na PDP ya samu kuri'u 20 inda ya doke abokin karawarsa John K Muva na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) wanda ya samu kuri'u 18.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng