Yanzu Yanzu: Kotu ta haramta wa Daily Nigerian wallafa bidiyon cin hanci na Ganduje
Wata babbar kotun Kano ta yi na’am da karar da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya shigar da ke neman a haramtawa jaridar Daily Nigerian da Jafaar Jafaar, mawallafinta, wallafa bidiyo a game da shi.
The Cable ta ruwaito cewa kafar watsa labaran ta wallafa wasu bidiy da ke nuna Ganduje yana karban cin hanci daga hannun yan kwangila.
Legit.ng ta tattaro cewa Ganduje ya nemi jaridar ta biya shi naira biliyan 3 akan bidiyon.

Asali: Depositphotos
Da take yanke hukunci a ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamba, kotu ta haramta wa Jafaar da Daily Nigerian wallafa ko yada bidiyon gwamnan har zuwa lokacin da za’a sake zama a ranar 6 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Buhari, Obasanjo, Atiku za su hade wajen kaddamar da littafin Jonathan a gobe
A baya mun ji cewa dan kwangilar daya baiwa gwamnan jahar Kano Abdullahi Umae Ganduje tare daukansa bidiyoya bayyana cewa a shirye yake ya gurfana gaban majalisar dokokin jahar Kano don zube musu hujjjojinsa game da sahihancin wannan bidiyo.
Majiyar Legit.com ta ruwaito dan kwangilar da bai bayyana sunansa ba ya bayyana ma majalisar burinsa na gurfana a gabansu ne cikin wata wasika da lauyansa Saeed Twada ya kai ma majalisar kafa da kafa, inda yace shi ne ya dauki Ganduje hoton, don haka yace akwai bukatar Ganduje ma ya bayyana.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng