Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP ba’a akan sakamakon zaben cike gurbi

Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP ba’a akan sakamakon zaben cike gurbi

Fadar shugaban kasa ta ce nasarorin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Asabar, 17 ga watan Nuwamba a jihohi uku alamu ne na abubuwan da zai faru a zaben 2019.

Jam’iyyar APC ta lashe mazabun tarayya uku a jihohin, Katsina, Kwara da Bauchi a zaben cike gurbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta gudanar.

Malam Garba Shehu, babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai a wani jawabi da ya turawa yan jarida a ranar Lahadi, 18 ga watan Nuwamba ya ce nasarar APC a jihohi uku ya tarwatsa hasashen jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na dawowa mulki a 2019.

Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP ba’a akan sakamakon zaben cike gurbi
Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP ba’a akan sakamakon zaben cike gurbi
Asali: Depositphotos

A cewarsa nasarar APC babban naushi ne ga masu yi wa PDP kamfen wanda suka yi ikirarin cewa an sauya ta, yan Najeriya ba za su taba manta barnar da suka bari ba a bayan 2015.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe jigon APC a Abuja, sun raunata uwargidansa da yara 3

Hadimin shugaban kasar ya yi godiya ga mutanen Katsina, Kwara da Bauchi kan goyon bayan da suka nunawa jam’iyya mai mulki a lokaci da bayan zaben cike gurbin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Mista Akeem Idoniboye, faston cocin Glorious Destiny Family Church, ya shawarci yan Najeriya da su fito su yi zaben 2019, domin su zabi shugabansu ba wai su tsaya suna addu’an Allah ya basu shugabanni na gari kawai ba.

Idoniboye ya bayar da sahawarar ne a wani taron addu’a a ranar Lahadi, 18 ga watan Nuwamba a Port Harcourt.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng