Atiku ko Buhari: Kungiyar kabilar Igbo ta yi karin haske a kan zabin dan takarar shugaban kasa

Atiku ko Buhari: Kungiyar kabilar Igbo ta yi karin haske a kan zabin dan takarar shugaban kasa

Kungiyar 'yan kabilar Igbo (Ohanaeze Ndigbo) ta musanta rahotannin dake yawo a gari cewar ta mika wuya tare da goyon bayan takarar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

Da ta ke mayar da martani a kan batun goyon bayan Atiku bayan kammala wani taro ranar Laraba a Enugu, kungiyar Ohanaeze ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar dan takarar da zata goyawa baya ba a zaben shekarar 2019.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun mataimakin sakataren yada labarai, Mazi Chuks, kungiyar ta yi watsi da rahoton cewar ta goyi bayan Atiku.

Sai dai kungiyar ta yi karin bayanin cewar duk da shugaban kungiyar, Cif John Nwodo, ya halarci taron da ya yi ranar Laraba a Enugu, hakan ba yana nufin cewar kungiyar ta bayyana cewar Atiku ne dan takarar ta ba.

Atiku ko Buhari: Kungiyar kabilar Igbo ta yi karin haske a kan zabin dan takarar shugaban kasa
Ziyarar Atiku ga 'yan kabilar Igbo
Asali: Depositphotos

"Kungiyar Ohanaeze ba ta zabi dan takara ba har yanzu, sabanin rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke watsawa.

DUBA WANNAN: Yaki sai da dabara: Buhari ya kaddamar da wani sabon wayon kamfen

"Babu hannun kungiyar Ohanaeze Ndigbo a shirya taron da Atiku ya yi da dattijai da ma su ruwa da tsaki 'yan kabilar Igbo na ranar Laraba duk da kasancewar shugaban mu, Cif John Nwodo, da wasu mambobi sun halarci taron.

"Taro ne na ganawa da jama'a da wasu abokan Atiku da Peter Obi su ka shirya.

"Sai dai maganar gaskiya shine mun ji dadin albishir din Atiku na cewar zai yiwa tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima idan ya zama shugaban kasa," a cewar jawabin Ohanaeze.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng