Yadda mutane su kayi wawason nama yayin da jirgin kasa ya markade shanu 10
Mutanen unguwar Kajola da ke Jihar Ogun sun kasance cikin murna a yayin da suka rika dibar nama suna kaiwa gidajensu sakamakon take wasu shanu 10 da jirgin kasa ya yi a yau Juma'a.
Maza da mata, har ma da masu sana'ar acaba sun rika zuwa da wukake da adduna inda suka rika yankan nama daga jikin shanun da sun riga sun mutu.
Jirgin kasan wanda ya taso daga Legas yana hanyarsa na zuwa tashan jirgin Kajola ne yayin da ya markade wasu shanu 10 da ke kokarin tsallaka layin dogon misalin karfe 11:50 na safiyar yau.
Shanun suna kiwo ne a kusa da titin jirgin kasan yayin da suka yi kokarin tsallakawa zuwa dayen bangaren.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Shari'ar Maryam Sanda: Shedu sun fadawa kotu yadda aka kashe Bilyaminu
Bisa ga dukkan alamu wadanda ke kiwon shanun ba su lura ba yayin da shanun suka hau kan titin jirgin.
Babu wani da adam da ya rasa ransa sakamakon hatsarin da ya afku.
Wasu magidanta da su kayi magana da manema labarai sun bayyana cewa masu kiwon shanun ba su daukar shawara domin an gargade su a kan kiwo kusa da layin dogon amma sunki su dena.
Sun kuma ce za ayi asarar naman ne muddin mutane ba su diba sunyi amfani da shi ba.
Wani magidanci mai suna Mr Adeola Paseda ya shaidawa The Nation cewa naman da ya diba zai ishe iyalinsa su rika ci har na tsawon mako daya.
"Ina daya daga cikin wadanda suka zo wajen da hatsarin ya faru; Naman da na samu zai usa iyali na amfani har na tsawon mako daya," inji shi.
Ba a ga masu shanun a inda hatsarin ya afku ba lokacin rubuta wannan rahoton.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng