Takaitaccen tarihin wata hazikar Yarinya 'Yar Najeriya mai suna Esther Okade

Takaitaccen tarihin wata hazikar Yarinya 'Yar Najeriya mai suna Esther Okade

Kwanakin baya ne Gidan Talabijin na CNN ta dauki labarin wata Yarinya ‘Yar Baiwa mai suna Esther Okade wanda tun tana ‘Yar shekara 10 da haihuwa ta ba Duniya mamaki saboda tsabar basirar ta da kuma kwarewa a harkar lissafi.

Takaitaccen tarihin wata hazikar Yarinya 'Yar Najeriya mai suna Esther Okade
Yarinya 'Yar Baiwa Esther Okade mai shirin zama Dakta a lissafi
Asali: UGC

Asalin Iyayen wannan Yarinya da aka haifa a Kasar Ingila ‘Yan Najeriya ne. Esther ta tashi a Garin Walsall ne a cikin tsakiyar Birtaniya inda tun tana shekara 10 ta shiga Jami’ar tafi-da-gidan ka watau Open University ta Kasar Birtaniyya.

Gidan yada labarai na CNN ta rahoto cewa Esther ta samu tarbiyya ne daga Mahaifyar ta. Tun Esther tana shekara 3 ta fara nuna bajintar da Allah yayi mata a harkar karatun Boko. Kwankwalwar wannan Yarinya dai ya zarce yadda aka saba ji.

Esther Okade ta saba kerewa sa’o’inta a aji, domin tun tana da shekaru 10 a Duniya ta lulu ta shiga kwaleji a wata Makarantar Ounsdale High School da ke cikin Garin Wolverhampton. A nan ne ta samu shaidar A-Level a bangaren ilmin lissafi.

KU KARANTA: Za a cigaba da daure wani tsohon Gwamnan Najeriya a kurkuku

A Jami’ar dai inda Esther ta ke karantar lissafi, ta ba kowa mamaki yayin da lashe jarrabawar da aka yi mata 100 bisa 100. Esther tace tana da sha’awar irin lissafin da ake koya masu domin tun tana karama Mahaifiyar ta ta ke yi mata darasi a gida.

Yanzu haka ma dai tana rubuta wani littafin koyon lissafi na kanana yara mai suna “Yummy Yummy Algebra." Okade tace tana da sha’awar ta fara Digirin ta na uku watau PhD a kan fannin “financial mathematics idan ta gama karatun Digirgir.

Mahaifiyar ta tace kafin Esther ta haura shekaru 4 da haihuwa ta kware a harkar algebra da kuma wani irin samfarin lissafi da ake cewa quadratic equations. Yanzu haka dai Mutane da-dama sun yi mamakin jin labarin wannan Yarinyar ‘Yar Baiwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng