Yanzu Yanzu: Kotu ta rage yawan shekarun da Jolly Nyame zai yi a gidan yari zuwa shekara 12
Kotun roko ta rage yawan shekarun da tsohon gwamnan jiharTaraba, Reverend Jolly Nyame zai yi a gidan yari daga shekara 14 zuwa shekara 12.
An kuma ci tarar Nyame naira miliyan 495 a hukuncin da kotu ta yanke a ranar Juma’a, 16 ga watan Nuwamba.
Hukuncin ya biyo bayan na farko da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a farkon 2018, inda aka yankewa Nyame shekaru 14 a gidan yari bayan an kama shi da laifin wadaka da naira biliyan 1.64 daga baitul malin jihar Taraba a lokacin da yake rike da mukamin gwamna.
KU KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya yi wa gwamnoni wankin babban bargo akan mafi karanci albashi 30,000
A baya Legit.ng ta rahoto cewa kotun daukaka kara da ke babban birnin tarayya Abuja da rage wa'adin zaman gidan yari da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Plateau, Joshua Dariye.
Kotun ta rage wa'adin daga shekaru 14 zuwa shekaru 10.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng