Anyi musayar zafafan kalamai tsakanin Oshiomhole da tsohon jigon APC kan zargin cin hancin $50m
Tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Timi Frank ya zargi shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da karban cin hancin dala miliyan 50 daga hannun yan takara daban-daban a lokacin zaben fidda gwani.
Frank ya yi zargincewa an biya mafi yawan kudin ne ga Oshiomhole ta jihohin Imo, Zamfara Adamawa da Ogun.
A wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 15 ga watan Nuwamba, Frank ya yi barazanar wallafa sunaye da adadin kudin da yan takara suka ba tsohon gwamnan na jihar Edo cin hanci domin ya wanke su sannan yam aye gurbin sunayen yan takarar da suka fadi da na wanda suka yi nasara.

Asali: Depositphotos
Amma da yake karyata zargin a matsayin mara tushe, Oshomhole ya bayyana Frank a matsayin dan siyasa mara na yi.
KU KARANTA KUMA: Idan hagu ta ki, sai ka koma dama don haka na bar APC na dawo PDP – Sanata Kwankwaso
Da yake Magana ta hannun babban sakataren labaransa, Simon Ebegbulem, ya kalubalanc Frank da ya wallafa sunayen wadanda suka bashi cin hanci ko kuma ya fuskanci shari’a.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng