‘Yan takaran PDP Atiku da Obi sun gana da Saraki da Kwankwaso

‘Yan takaran PDP Atiku da Obi sun gana da Saraki da Kwankwaso

- Kwamitin yakin neman zaben Atiku sun yi wani zama a cikin Abuja

- Atiku, Obi, Kwankwaso da Saraki sun yi taro ne game da zaben 2019

- An hangi wasu Gwamnoni irin su Mr. Udom Emmanuel a wajen taron

‘Yan takaran PDP Atiku da Obi sun gana da Saraki da Kwankwaso
Atiku ya zauna da su Saraki da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: UGC

Mun samu labari cewa ‘Dan takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kuma manyan PDP irin su Rabiu Musa Kwankwaso a Birnin Tarayya Abuja.

‘Dan takaran Shugaban kasar yayi wani zama na musamman ne tare da kwamitin yakin neman zaben sa wanda Bukola Saraki yake jagoranta. Abokin takarar Atiku, Mista Peter Obi yana cikin wadanda su ka halarci wannan taro.

KU KARANTA: Zan fitar da sunayen wadanda su ka ba Oshiomhole cin hanci - Tsohon kakakin APC

Sauran wadanda su ka yi takarar kujerar Shugaban kasa a PDP da Atiku irin su Ibrahim Dankwambo, David Mark, Jonah Jang, su na cikin wadanda su ka halarci wannan zama da aka yi a cikin dare kamar yadda mu ka ji.

Mun ga shi kan sa Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Prince Uche Secondus da wasu manyan Jagororin Jam’iyyar a wajen taron. Wani Hadimin Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya fitar da hotunan zaman.

Kwanan nan ne dai Atiku ya dawo Najeriya bayan ya tafi Kasar UAE inda ya shakata ya kuma rika gudanar da taro daban-daban domin ganin yadda PDP za ta fuskanci APC a zaben da za ayi a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng