Musulman kabilar Igbo sun gabatar da bukatar su ga Buhari

Musulman kabilar Igbo sun gabatar da bukatar su ga Buhari

Kungiyar musulman yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo (SEMON) ta bukaci shugaba Buhari da kar ya saurara a yakin da ya ke yi da cin hanci da karya tattalin arziki duk da kasancewar zaben shekarar 2019 na kara matsowa.

A wani jawabi da SERMON ta fitar bayan kammala wani taro na kwana guda ta bukaci shugaba Buhari ya yi amfani da cancanta ba kabila ba wajen nada mukaman siyasa.

Taron da SERMON ta yi a babban masallacin Abuja ya samu halartar manyan 'yan kabilar Igbo musulmi da ke cikin gwamnati da kuma harkokin kasuwanci.

Musulman kabilar Igbo sun gabatar da bukatar su ga Buhari
Musulman kabilar Igbo sun gabatar da bukatar su ga Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani dan majalisa ya sake ficewa daga APC, ya bayar da dalilai

Bayan jaddada goyon bayanta ga shugaba Buhari, kungiyar ta bukaci gwamnonin yankin 'yan kabilar Igbo da su kula da hakkin Musulmin yankin, kasancewar ba su da yawa.

Kazalika kungiyar ta bukaci 'ya'yanta da su shiga fagen siyasa domin a dama da su, musamman a bangaren shiga takarar kujerun gwamna da kuma majalisar tarayya da kuma ta jihohi.

"Muna yabawa kokarin shugaba Buhari na kawo canje-canje ma su amfani a Najeriya. Kiran mu gare shi shine kar ya saurara a yaki da cin hancin da yake yi sannan mu roke shi da ya ke bawa cancanta fifiko a nadin mukaman siyasa.

"Muna yi masa addu'o'in fatan alheri kuma za mu cigaba da bashi goyon baya.

"Muna yiwa Najeriya addu'ar samun kwanciyar hankali da hadin kan jama'a tare da yin kira ga 'yan siyasa da su zama ma su biyayya ga tsarin doka a wannan lokaci da mu ke tunkarar zaben shekarar 209," kamar yadda ya ke a jawabin SEMON.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng