Ku daina amfani da matasa a matsayin Karen farauta – Obasanjo ga yan siyasa
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a ya gargadi yan siyasa a Najeriya akan amfani da matasa a matsayin Karen farauta
- A cewarsa su suna killace yaransu a tsararren wuri da makarantu sannan su yi amfani da yaran talaka wajen ta da zaune tsaye
- Obasanjo ya marawa gyara kundin tsarin mulkin baya wanda ya ba matasa damar shiga harkar siyasa
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, a jiya, Laraba, 14 ga watan Nuwamba ya gargadi yan siyasa a Najeriya akan amfani da matasa a matsayin Karen farauta, yayinda suke boye nasu ‘ya’yan a killataccen wuri.
A wata sanarwa a Abeokuta daga hadiminsa, Kehinde Akinyemi, tsohon shugban kasar yayi mgana a birnin Landan wajen kaddamar da kwalejin King’s College London Global Leaders Engagement Series.

Asali: Instagram
A cewarsa: “Ya ishe ku yin amfani da yayan mutane a matsayin Karen farauta yayinda muke killace namu a aljannah.
"Ya ishe ku amfani da yayan mutane a matsayn masu kwato akwatunan zabe, yayinda namu ke tsadaddun makarantu."
KU KARANTA KUMA: Mutanen Najeriya na neman Kasar Amurka ta binciki Atiku kafin zaben 2019
Tsohon shugaban kasar ya marawa gyara kundin tsarin mulkin baya wanda ya ba matasa damar shiga harkar siyasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng