CBN ta saka jarin $210m a kasuwar canjin kudi

CBN ta saka jarin $210m a kasuwar canjin kudi

A jiya ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ta sanar da cewar ta saka karin zunzurutun kudi $210 a cikin kasuwanin canji na bankunan kasa da kasa.

Alkalluman da CBN ta fitar ya nuna cewa bangaren manyan dilalai na canji sun samu $100 miliyan yayin da bangaren kananan kamfanoni da masana'antu sun sami $55 miliyan sanna an saka $55 miliyan a wata bangaren kasuwar.

Direkan sashin hulda da jama'a na bankin, Isaac Okafor ya bayar da tabbacin cewa bankin za ta cigaba da saka jari a kasuwar na canji domin inganta hada-hadan kudade.

CBN ta kara jarin kasuwar canjin kudi na $210m
CBN ta kara jarin kasuwar canjin kudi na $210m
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata soja ta sheke dan sanda da mari bayan ya kawo mata wargi

Ya kuma yi albishir da cewa bisa ga dukkan alamu darajan Naira za ta cigaba da karuwa a kan dalla da ma wasu kudaden manyan kasashen waje saboda yadda abubuwa ke tafiya dai-dai a kasuwar ta Najeriya.

A ranar Juma'a 2 ga watan Nuwamban 2018, babban bankin na kasa ta saka bayar da tallafin $337.16 miliyan a (SMIS) da CNY 56.17 miliyan domin inganta cinnikaya a kasuwanin canjin.

A jiya Talata 13 ga watan Nuwamban 2018 ana musayar $1 da N360 a kasuwanin canjin na kasa da kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164