Shugaba Buhari ya bada kwangilar gadar 2nd Neja a kan kudi Biliyan 206 – Fashola
Mun samu labari daga Jaridun Najeriya cewa Gwamnatin Tarayya ta dawo da maganar aikin babban gadar nan ta “2nd Niger” inda yanzu har an ba wani kamfani kwangilar yin wannan gagarumin aiki.

Asali: Depositphotos
Ministan gidaje da harkar wutan lantarki da kuma ayyuka na Najeriya, Babatunde Fashola ya bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta bada kwangilar a wajen zantawa da yayi da ‘Yan jaridu a Ranar Litinin dinnan a Garin Abuja.
Raji Babatunde Fashola ya bayyana cewa za a kammala aikin ne a cikin watanni 36. Ministan har ila yau, ya bayyana mana cewa gidauniyar nan da aka kafa domin gina abubuwan more rayuwa ta PIDF ce za ta saki kudin aikin.
KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta na shirin ginawa Ma’aikatan Najeriya gidaje 60, 000
Fashola yace za a kammala aikin Legas zuwa Ibadan da kuma hanyar Abuja zuwa Zaria har Kano ne ta wannan tsari na PIDF. Ministan yace hakan zai sa kudi ba zai taba yankewa lokacin da ake tsakiyar yin wannan ayyuka ba.
A game da gadar nan da ta hada Yankin Neja-Delta da sauran Kudancin Najeriya, Ministan yace za a dawo bakin aiki gadan-gadan a yanzu. Fashola yace damina yana cikin abin da ya sa aka dakatar da aikin saboda zurfin ruwa.
An dai ba kamfanin nan na Julisu Berger wannan aiki ne a kan kudi Naira Biliyan 206 inji Ministan. Dama can kamfanin nan na Julius Berger ne su ka soma aikin sai dai an dade ba a kai ko ina ba kafin zuwa Gwamnatin nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng