Za mu karasa gine-ginen gidajen Gwamnatin da mu ke yi – Fashola

Za mu karasa gine-ginen gidajen Gwamnatin da mu ke yi – Fashola

Mun ji cewa Ministan ayyuka da gidaje da kuma harkar wutan lantarki na Najeriya, Babatunde Raji Fashola ya tabbatar da cewa Gwamnati za tayi bakin kokari wajen karasa ayyukan gidajen da ta ke yi.

Za mu karasa gine-ginen gidajen Gwamnatin da mu ke yi – Fashola
Gwamnatin Shugaba Buhari ta na gina gidaje a fadin Najeriya
Asali: Depositphotos

Babban Ministan ya tabbatar mana da wannan ne a lokacin da ya kai ziyara Jihar Kano domin kaddamar da wani shiri da babban bankin da ke bada jinginar gida a Najeriya ya shirya a Ranar Talata 13 ga Watan Nuwamban nan.

Wani babban Jami’i a Ma’aikatar na ayyuka da gidaje da wutan lantarki, Onaeko Temitope Olayinka, ne ya wakilci Ministan Kasar a taron da za ayi kwanaki 4 ana yi. Darektan yace Gwamnatin nan za ta kammala gine-ginen da ta soma.

A madadin Ministan, Temitope Olayinka ya nemi babban bankin ya kara maida himma wajen maida kudin da ya kashe a kan gine-ginen kananan gidaje domin Ma’aikatan Gwamnati. Jami’in ya nemi bannkin ya hada kai da irin su NLC.

KU KARANTA: Ayyukan Buhari na shekaru 3 su na neman zarce abin da PDP tayi - Fashola

Shugaban wannan banki da ke bada jinginar matsuguni, Arc. Ahmed Dangiwa ya bayyana cewa yanzu sun maida fiye da Naira Biliyan 3 daga kudin da su ke bi bashi inda kuma ake sa ran tatso kudi har Naira Biliyan 43 a shekarar badi.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo tsarin da zai sa a ginawa Ma’aikata sama da 60, 000 gidaje a fadin kasar inda kuma za a samawa dubunnan daruruwan mutane aikin yi. Za a kashe Biliyoyin Nairori ne wajen wannan gagarumin aiki a Kasar.

Bankin na shan wahalar maida kudin da ya kashe wajen gina gidajen Ma’aikata kafin zuwa Gwamnatin Buhari inda har ta kai ana maka wadanda su ka saba yarjejeniyar da aka yi a gaban Hukumomin EFCC da ICPC da ke maganin miyagu a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng