An kama wani basarake bayan samunsa da cuwa-cuwa wajen sayar da filaye
Jami'an yan sandan Najeriya sun damke Sarkin kauyen Ferowa da ke karamar hukuma Ifo da ke jihar Ogun, Muyideen Folorunso bisa zarginsa da damfarar wani mutum da ya sayar masa fili a kan kudi N15.5 miliyan.
Kakakin 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa an kama basaraken ne a ranar Talata bayan kamfanin da ya sayarwa filin sun shigar da kara a caji ofis.
"An kama shi ne bayan wanda ya sayarwa mahukunta Jaxmat Homes and Properties sun saya fili mai girman acre 23 wajen basaraken a kan kudi N15.5 miliyan kuma an biyashi amma daga bisani ya fara sayar da wani sashi filin ga wasu mutane," inji Oyeyemi.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: An rufe wata makaranta a kudancin Najeriya saboda wasu dalibai sun saka hijab
An gano cewa Folorunso ya sayar da acre 17 cikin 23 ga wasu mutane daban wanda hakan yasa kamfanin da shigar da kara wajen 'yan sanda.
"Bayan shigar da karar, Kwamishinan yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu ya bukaci jami'in da ke kula da korafe-korafen mutane ya bincika batun kuma ya gayyato wanda ake zargin," a cewar Oyeyemi.
A cewar Kakakin yan sandan, Mr Folorunsho ya amsa cewar ya karbi kudi daga wakilan kamfanin kuma ya sayar musu da fili sai dai daga bisani ya fara sayar da wani bangare na wasu filayen ne ga wasu mutane domin yana bukatar kudin bikin nadin sarautarsa.
Za a gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng