Majalisar wakilai na daf da zartar da doka a kan kisa, safara da cin naman Jakai
A yau, Talata, ne kudirin da ke neman a hana fitar da jakai tare da cin namansu ya samu tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.
Kudirin da dan majalisa Garba Muhammed (dan jam'iyyar APC daga jihar Kaduna) ya dauki nauyin gabatar da shi a gaban majalisa, na son a haramta kisa tare fitar da jakai daga Najeriya domin gudun kar jinsin dabbar ya bace a Najeriya.
Kazalika dan majalisar ya yi sharhi a kan tsohon tarihi da jaki ke da shi a rayuwar mutane, musamman ta fuskar sufuri da kasuwanci a yankunan karkara.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi
"Adadin Jakan da ke kasar nan ya ragu matuka a 'yan kwanakinnan. Hakan na da alaka da safarar Jakan da ake yi zuwa kasar China daga kasashen nahiyar Afrika ta yamma.
"Kasar China na sayen Jaki da daraja saboda ana samun sindarin "gelatin" da ke taimakon jini da inganta garkuwar jiki a jikin fatar sa.
"Bayan haka, naman jaki na daga cikin abincin kwalam a yankin gabashin kasar China. Lamarin da ya saka 'yan China ke rububin saye Jakan da ke yankin Afrika ta yamma," a kalaman dan majalisar.
Da yake bayar da misali, Muhammed ya bayyana cewar Jakin da a baya bai fi Naira N15,000 zuwa N18,000 ba, yanzu ana sayar da shi a kan kudi N70,000 zuwa N75,000. Lamarin da ya ce ya sa Jaki ya fi karfin tattalin arzikin talaka.
"Idan mu ka yi shiru, mu ka zuba ido, watarana za mu wayi gari ba mu da jakai da za a yi amfani da su domin sufuri ko a dakin gwaje-gwaje na kimiyya."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng