Hukumar Hisbah Ta Dawo Kan Mata a Jihar Katsina, an Kafa Dokar Hana Talla

Hukumar Hisbah Ta Dawo Kan Mata a Jihar Katsina, an Kafa Dokar Hana Talla

  • Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta haramta wa ’yan mata yin tallace-tallace da daddare daga karfe 10 na dare a fadin jihar
  • Kwamandan hukumar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ya ce matakin na da nufin kare ’yan mata daga cin zarafi
  • Hisbah ta kuma yi gargadi kan sake bude gidajen karuwai, tallata magungunan gargajiya da kalaman batsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta sanya dokar hana ’yan mata gudanar da sana’ar tallace-tallace da daddare.

Hukumar ta umarci a dakatar da duk wani aikin sayar da kaya daga karfe 10:00 na dare a dukkan sassan jihar.

Hisbah ta hana mata talla a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda da shugaban Hisbah, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa. Hoto: Dikko Umaru Radda, Mudassir Umar Jarumi.
Source: Facebook

Kwamandan hukumar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi jama'a ya sheƙa barzahu a Katsina

Ya ce an dauki matakin ne domin kare rayuka da mutuncin ’yan mata daga barazanar cin zarafi da kuma tabbatar da bin ka’idojin addinin Musulunci.

Ya bayyana cewa dokar za ta shafi tashoshin mota, kasuwanni da sauran wuraren da ake gudanar da harkokin tallace-tallace a fadin jihar.

Dalilan da suka sa Hisbah ta dauki matakin

A cewar kwamandan, hukumar ta samu rahotannin cewa wasu daga cikin ’yan matan da ke yawo suna sayar da kaya cikin dare na fuskantar matsaloli daban-daban.

Ya ce wasu na shiga ayyukan da suka saba koyarwar addinin Musulunci, yayin da wasu kuma ke fuskantar cin zarafi ta hanyar fyade.

Sheikh Saifullahi ya bayyana cewa hukumar ba za ta lamunci irin wadannan abubuwa ba, saboda sun saba wa koyarwar Musulunci.

Ya kara da cewa za a tura jami’an Hisbah zuwa muhimman wurare, musamman kasuwanni da tashoshin mota, domin tabbatar da cewa an bi wannan doka.

Haka kuma, ya gargadi iyaye da su daina barin ’ya’yansu mata suna yawo suna tallace-tallace a lokutan dare, yana mai bukatarsu da su dauki nauyin kula da lafiyarsu da tsaronsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je har gida sun harbe shugaban Miyetti Allah

An sanya ido kan masu magungunan gargajiya

A wani bangare na jawabin, kwamandan ya sanar da cewa hukumar za ta fara sa ido kan ayyukan masu sayar da magungunan gargajiya domin tabbatar da cewa tallace-tallacensu ba su saba wa koyarwar Musulunci ba.

Ya nuna damuwa kan yadda wasu masu sana’ar ke amfani da kalaman batsa da maganganu marasa tarbiyya wajen tallata magungunansu, ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta sake lamuntar irin wannan dabi’a ba.

An hana mata tallar dare a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An gargadi masu gidajen karuwai da giya

Haka kuma, Sheikh Saifullahi ya ce hukumar Hisbah ta samu bayanai kan sake bude wasu gidajen karuwai a wasu sassan jihar.

Saboda haka, ya umarci masu gudanar da irin wadannan wurare su rufe su, ko kuma su fuskanci matakin shari’a.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu dokar hana sayar da giya, musamman barasa, tana nan daram a jihar Katsina.

Kwamandan ya gargadi masu wannan sana’a da su guji sayar da giya a wuraren da jama’a ke taruwa.

Kara karanta wannan

Barayi sun shiga masallaci sun sace fankoki sama da 20 a Kano

A karshe, ya bukaci al'ummar jihar, musamman Musulmi, su bai wa hukumar hadin kai wajen gudanar da ayyukanta.

Ya ce ba a kafa Hisbah domin gallaza wa jama’a ba, sai dai domin tabbatar da bin koyarwar Musulunci bisa tanade-tanaden dokokin da suka kafa hukumar.

Hisbah ta rufe otal a Katsina

A baya, an ji cewa Hukumar Hisba a Katsina ta fusata kan yadda wani otal ya yi fatali da yarjejeniyar da gwamnatin jihar.

Hukumar ta bayyana cewa ta rufe otal din New Palace ne saboda ba wannan ne karon farko da aka gano yara kanana sun kama daki a cikinsa ba.

Sheikh Aminu Usman ya shaida cewa sai da su ka dade su na jan kunnen hukumomin otal din, amma sai ga shi an gano wasu yara mata kanana biyu sun kama daki yayin samamensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.