Idan ku na so mu binciki Tinubu ku rubuto mana takarda – Inji Magu
- Shugaban EFCC Ibrahim Magu ya nemi a rubuta korafi idan ana nema a binciki Asiwaju Bola Tinubu
- Kwanaki aka ji Bola Tinubu yana cewa ya fi Jihar Osun arziki don haka aka nemi Magu ya kama sa
- Magu ya fadawa ‘Yan jarida su kawo masa duk takardun da ake bukata su ga yadda zai yi da Tinubu

Asali: Depositphotos
Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa watau Ibrahim Magu ya shawarci wani ‘Dan Jarida ya rubuta korafi ga EFCC idan yana da sha’awar ganin an binciki Bola Tinubu.
Shugaban Hukumar ta EFCC ya nemi a aiko masa takarda ta tuhuma muddin ana son samun karin bayani game da yadda Asiwaju Bola Tinubu ya mallaki dukiyar sa. Bola Tinubu yana cikin manyan APC kuma na hannun daman Buhari.
KU KARANTA: An kama ‘Dan takaran APC da laifin handame makudan Miliyoyin Daloli
Ibrahim Magu yayi wannan jawabi ne bayan wani ‘Dan Jarida yayi masa tambaya game da babban Jigon Jam’iyyar APC watau Bola Tinubu wanda yayi ikirarin cewa dukiyar sa a Duniya ta zarce abin da Jihar Osun ta mallaka gaba da baya.
Magu ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa idan har su na so su ka ga Hukumar EFCC ta yi wani bincike, dole su aiko masu takarda dauke da duk bayananan da ake bukata, Magu yace ba wai kurum za su biyewa surutan da ake yi a gidajen Rediyo bane.
Shugaban EFCC Magu ya bayyana wannan ne a lokacin da yake bikin murnar cikin sa shekaru 3 yana aiki. EFCC ta kuma yi magana game da dawowa da shari'ar tsohuwar Minista Deziani Alison-Madueke Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng