Babban bankin Najeriya ta bayyana wadanda suka fi taurin bashi tsakanin Maza da Mata
Babban bankin Najeriya ta bayyana cewa sau dayawa Mata sun fi Maza biyan bashi a Najeriya, don haka tayi kira ga Mata dasu garzayawa bankuna domin karbar kanana da matsakaitan bashi, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.
Majiyar Legit.com ta ruwaito daraktan watsa labaru na CBN, Isaac Okorafor ne ya bayyana haka a yayin wani taro da babban bankin ta shirya a jahar Legas a kasuwar duniya dake Legas a ranar Juma’ar da ta gabata.
KU KARANTA: Wasu gagararrun yan fashi da makami sun gamu da mummunar ajali a hannun Yansanda
A cewar Okorafor, Mata sun fi maza biyan bashi, ma’ana Maza sun fi mata taurin bashi, ta yadda idan bankuna suka basu bashi da kyar da sudin goshi zasu dawo da wadannan kudade, don haka yace bankuna sun fi son baiwa mata rancen kudi.
Bugu da kari Okorafor yace da wannan dalili ne CBN ta baiwa mata muhimmanci a wajen daukan aiki, inda ta kara adadin matan dake aiki a CBN a daukan aikin da ta yin a kwana kwanannan.
“Muna baiwa mata muhimmanci sosai, kuma mun kara adadin mata dake aiki a CBN saboda mun tabbatar mata sun fi kokari, sun fi nuna hazaka, sun fi iya kasuwanci kuma sun fi aminci wajen harkar kudi.
“Ya fi sauki ka baiwa mata bashin kudi saboda suna biya, su ba kamar maza bane, wadanda basu da tabbacin biyan bashin kudin da aka basu, idan macece keda kudi, ai anfi ganin amfanin kudin fiye da namiji.” Inji shi.
Sai dai Okorafor yayi nuni da cewa duk da cewa mata sun fi iya juya kudi, amma basu cika zuwa neman rancen kudi daga banki ba, ire iren bashin da bankuna ke baiwa kananan da matsakaitan sana’o’I, wadanda suka nufi bankunan kuma basu da tsari da kadarorin da ake bukata.
Bugu da kari Daraktan yace da dama daga cikin matan kuma basu da asusun banki inda za’asa musu kudaden, don haka yace CBN na kokarin baiwa mata karfin gwiwa don su samu saukin karbar basussukan.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng