Wasu gagararrun yan fashi da makami sun gamu da mummunar ajali a hannun Yansanda

Wasu gagararrun yan fashi da makami sun gamu da mummunar ajali a hannun Yansanda

Wasu gungun gagararrun yan fashi da makami sun gamu da ajalinsu a hannun wasu jaruman jami’an Yansandan Najeriya a yayin wata musayar wuta da suka yi a tsakaninsu a ranar Lahadi 11 ga watan Nuwamba a jahar Taraba.

Majiyar Legit.com ta ruwaito an yi wannan batakashi ne akan hanyar kamfanin abincin dabbobi na Kwassa dake cikin karamar hukumar Bali na jahar Taraba, inda Yansandan suka kashe yan fashin guda uku, tare da jikkata sauran.

KU KARANTA: Alhamdulillah: Wani fitaccen malamin jami’a a Arewa ya binciko maganain cutar daji

Kwamishinan Yansandan jahar Taraba, David Akinremi ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace bayan artabun da yayi sanadiyyar mutuwar yan fashi da makami guda uku, sun gano bindiga da alburusai, wuka da layoyi daga wajensu.

“Da misalin karfe 9:30 na safiyar Lahadi ne muka samu labarin wasu gungun yan fashi da makami sun tare hanyar da tashi zuwa kamfanin abincin dabbobi na Kwassa dake cikin karamar hukumar Bali, nan da nan muka aika da tawagar Yansanda.

“Amma daga hangen Yansandanmu, sai yan fashin suka bude musu wuta, nan take yansandan suka mayar da biki, anan aka fara musayar wuta tsakanin Yansanda da yan fashin, inda muka samu nasarar kashe guda nan take, biyu kuma suka mutu a hanyar asibiti sakamakon raunin da muka yi musu.

“Daga cikin abubuwan da muka gano daga wajen yan fashin akwai bindiga, alburusai, wuka, fuskar badda kama, da kuma wasu layoyin tsafe tsafe.” Inji Kwamishina Akinremi.

Daga karshe kwamishinan Yansandan yace sun baza komarsu don tabbatar da sun kamo sauran yan fashin da suka tsere cikin daji da raunin bindiga daban daban.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng