Sabon harin Boko Haram a Maiduguri: An kashe mutum, an kone gidaje

Sabon harin Boko Haram a Maiduguri: An kashe mutum, an kone gidaje

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce an kashe mutum guda tare da kona gidaje 65 a sabon harin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai unguwar Bale-Shuwa da ke garin Maiduguri, jihar Borno.

Sabon harin Boko Haram a Maiduguri: An kashe mutum, an kone gidaje
Sabon harin Boko Haram a Maiduguri: An kashe mutum, an kone gidaje
Asali: UGC

A yau, Lahadi, ne shugaban hukumar NEMA na yankin arewa maso gabas, Bashir Garba Idris, ya tabbatar da rahoton kai harin.

Ya bayyana cewar mayakan kungiyar Boko Haram din sun yi awon gaba da dabbobi fiye da 500.

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Garba ya kara da cewar an bawa wadanda su ka samu raunuka agajin gaggawa tare da fara kokarin samun kiyasin asarar da mazauna yankin su ka yi domin gaggauta ba su kayan agajin gaggawa.

Wani rahoto ya bayyana cewar dakarun soji da hadin gwuiwar civilian JTF sun dakile harin kafin ya yi muni.

An samu yawaitar harbe-harbe da fashewar sinadarai a yankin, lamarin da ya tilasta mazauna unguwar tserewa cikin kwaryar birnin Maiduguri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel