Godwin Udo Udo da wasu manyan 'Yan PDP sun koma APC a Akwa Ibom

Godwin Udo Udo da wasu manyan 'Yan PDP sun koma APC a Akwa Ibom

- Jam’iyyar PDP ta gamu da wani babban rashi kwanan nan a Jihar Akwa Ibom

- Wani Jigon Jam’iyyar, Godwin Udo Udo ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC

- Udo yace zai yi kokarin ganin Jam’iyyar APC ta kawo Jihar Akwa Ibom a 2019

Godwin Udo Udo da wasu manyan 'Yan PDP sun koma APC a Akwa Ibom
PDP ta rasa dinbin magoya-bayan ta a Jihar Akwa Ibom
Asali: Depositphotos

Labari ya zo mana cewa Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta samu dinbin sababbin Magoya-baya a Ranar Juma’ar nan a Jihar Akwa Ibom a Yankin Kudu maso Kudancin Najeriya inda Jam’iyyar adawa ta PDP ke da karfi sosai.

Kamar yadda mu ka ji, Jam’iyyar PDP ta rasa wani babban Jigon ta a Jihar Akwa Ibom watau Dr Godwin Udo Udo a Ranar Juma’a 9 ga Watan Nuwamban nan ne. Godwin Udo Udo ya fice daga Jam’iyyar ya sauya-sheka zuwa APC.

Udo Udo wanda yana cikin Jagororin PDP a Karamar Hukumar Ini ya sanar da ficewar sa daga Jam’iyyar zuwa APC a wajen wani taro da aka shirya a cikin Mbiabong Ikot Udofia. Ini Okopido ne ya karbi sababbin ‘Ya ‘Yan na APC.

KU KARANTA: Wani Gwamnan APC ya gama shirin tserewa daga jam'iyyar

Kwanakin baya ne dai wasu manyan ‘Yan siyasa daga Garin na Ini irin su Obong Otu Robert Akpan da kuma wani tsohon ‘Dan Majalisa Farfesa Ini Udoka su ka tsere daga Jam’iyyarPDP. Udo yace za su yi APC aiki sosai a zaben 2019.

Udo Udo ya sha alwashin hada-kai da tsohon Shugaban NBC na kasa watau Obong Akpan wajen ganin Jam’iyyar APC ta tika PDP da kasa a zabe mai zuwa. ‘Dan takarar Gwamnan Jihar a APC yace Jam’iyyar ta kara karfi a Akwa Ibom.

Yanzu haka dai ana ta gamuwa da sauye-sauyen sheka iri-iri a Jihar ta Akwa-Ibom yayin da ake shirin 2019. Ficewar tsohon Gwamna Sanata Godswill Akpabio daga PDP ne dai duk ya haddasa wannan a Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng