Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki

Labari ya zo mana daga Jaridar nan ta Daily Trust cewa sohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki a halin yanzu inda yace mutane da-dama su na cikin wani kangi.

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki
Obasanjo yace wasu sun fusata sun cire rai da Najeriya amma su kara hakuri
Asali: Twitter

Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa Jama’an Najeriya sun shiga wani hali na fusata da mugun takaici ganin yadda Kasar ta ke ciki. Obasanjo ya bayyana wannan ne a babban dakin karatun sa na OOPL da ke cikin Jihar Ogun.

Obasanjo yace Ubangiji bai kirkiri Najeriya domin a wahala ba, sai dai domin ta cigaba kamar sauran manyan Kasashen Duniya. Tsohon Shugaban ya fadawa jama’a su kara hakuri da Najeriya duk da yadda abubuwa su ka tabarbare.

KU KARANTA: An raba gari: Yaron wani Hadimin Jonathan ya bi jirgin yakin Buhari

Tsohon Shugaban na Najeriya ya karbi ziyarar ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Ogun a karkashin Jam’iyyar ADC Gboyega Nasiru Isiaka ne a cikin Oke-Mosan da ke Garin Abeokuta. Cif Obasanjo yace abubuwa za su gyaru nan gaba a Najeriya.

Tun kwanaki dai Obasanjo ya fara kira ga al’ummar kasar su hada-kai wajen ganin sun ceto Najeriya. Obasanjo yace an yi kura-kurai da yawa a baya a kasar wanda su ka nemi su raba kan kasar amma aka yi nasarar hakan bai yiwu ba.

Dazu mu ka ji labari cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron kasa da kasa da za ayi a kan zaman lafiya tsakanin Ranar 11 zuwa 13 ga watan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng