Rikicin kudin haraji: Kamfanin MTN ta maka gwamnatin tarayya gaban Kotu

Rikicin kudin haraji: Kamfanin MTN ta maka gwamnatin tarayya gaban Kotu

Kamfanin sadarwa ta MTN ta maka gwamnatin tarayya gaban babbar kotun tarayya dake jahar Legas inda take kalubalantar gwamnatin tarayya game da wasu makudan kudade; naira biliyan 242 da dala biliyan 1.3 da gwamnatin ta daura mata a matsayin haraji.

Majiyar Legit.com ta ruwaito MTN ta nemi Kotu ta tursasa ma gwamnatin tarayya ta biyata kudi naira biliyan uku sakamakon asarar data yi a sanadiyyar bin kadin harajin da gwamnati ta sanya mata, wanda a cewarta bata san da shi ba.

KU KARANTA: Tsohon Soja ya halaka mutane 12 a harbin mai kan wuya a gidan giya

A karar da MTN ta shigar gaban kotun, ta kalubalanci halaccin babban alkalin gwamnati dangane da bibiyan harajinta da yake yi tun daga 2007 zuwa yanzu, musamman harajin fito, da kuma wanda ake kara ma kaya (VAT), wanda suka kai naira biliyan 242 da dala biliyan 1.3.

Haka zalika MTN ta bayyana ma kotu cewa binciken da babban lauyan kotun tarayya yayi ya saba ma sashi na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka tace babban lauyan ya yi azarbabi wajen wuce gona da iri, tunda batun haraji aikin ne na hukumar kwasatma da hukumar FIRS.

Bugu da kari MTN ta bukaci Kotun ta haramta ma babban lauyan Najeriya cigaba da gudanar da binciken akan cewa an shiryatane da wata muguwar manufa, tare da yin watsi da duk wasu rahotanni da binciken ta bankado.

Sai dai shima babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami SAN ya musanta tuhume tuhumen da MTN ke yi masa, inda yace kamata ya yi kotu ta yi watsi da wannan kara na MTN saboda yah aura watanni 3, wanda shine iyakan lokacin da doka ta tanadar a shigar da karar duk wani jami’in gwamnati.

Don haka a cewarsa MTN ta fara wannan rikicin sharia ne da kafar hagu, ta hanyar yin kaca kaca da sashi na 2 na dokokin kare jami’an gwamnati, wanda yace duk wata kara da za’a shigar da jami’in gwamnati kada ta wuce watanni uku daga lokacin da ya aikata laifin.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkalin kotun, Chukwujekwu Aneke ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Disamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel