Allah yayi: Madugun Kwankwasiyya ya shigo cikin Garin Kano

Allah yayi: Madugun Kwankwasiyya ya shigo cikin Garin Kano

Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya iso Garin Kano jiya inda ake sa ran zai shiryawa babban zabe mai zuwa na 2019 da za ayi a farkon shekara mai zuwa.

Allah yayi: Madugun Kwankwasiyya ya shigo cikin Garin Kano

Sanata Kwankwaso zai yi sallar Juma'a a cikin Kano yau
Source: UGC

Rabiu Musa Kwankwaso wanda yanzu haka yake wakiltar Kano ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya dade bai zuwa Mazabar ta sa bayan ya samu matsala da Magajin sa kuma tsohon Mataimakin sa Gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje.

Yanzu haka dai Sanatan yana gidan sa da yake titin Miller a cikin Unguwar Bompai a cikin Birnin Kano. Ana tunani cewa babban ‘Dan siyasar zai dade a cikin Jihar Kano kafin ya koma Birnin Tarayya kamar yadda mu ka samu labari.

KU KARANTA: Ana shirin fatattako ‘Daliban Kano da Kwankwaso ya tura karatu a kasar waje

Ana dai sa rai za a fara yakin neman zabe ne a Najeriya nan da wasu ‘yan kwanaki. Tsohon Gwamnan zai yi kokarin ganin ‘Dan takarar PDP watau Abba Kabir Yusuf yayi nasara a zaben Gwamnan Jihar Kano da za ayi a 2019.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana cikin wadanda su ka nemi kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP amma ya sha kashi a hannun Atiku Abubakar. Yanzu dai Sanatan zai yi kokarin ganin aakalla PDP ta karbi mulki a Kano.

Kwankwaso yayi kokarin ba Surukin sa takara a PDP wanda hakan ya sa ya rasa wasu manyan ‘Yan Kwankwasiyya inda shi kuma Salihu Sagir Takai ya fice daga Jam’iyyar ya koma Jam’iyyar PRP domin yin takara a zaben badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel