Kotu aika barawon babur zaman gidan yari na wata 12

Kotu aika barawon babur zaman gidan yari na wata 12

Wata kotu da ke zamanta a Mararaba a jihar Nasarawa ta yanke hukuncin zaman gidan yari na watanni 12 kan wani mutum mai suna Shagari Ali mai shekaru 36 a duniya bayan samunsa da laifin satar babur wadda kudinta ya kai N150,000.

Alkalin kotun, Mr Ibrahim Shekarau ya yanke hukuncin ne bayan wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa ba tare da wata jayaya ba.

Sai dai alkalin ya kuma bashi zabin biyan tarar N18,000 sannan ya gargadi shi da ya dena aikata laifuka bayan ya fito daga gidan yarin.

Kotu aika barawon babur zaman gidan yari na wata 12
Kotu aika barawon babur zaman gidan yari na wata 12
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnan Najeriya ya karaya, ya ce Allah ne kadai zai iya da Najeriya

Shekarau ya kuma umurci wanda aka yankewa laifin ya biya N20,000 ga wanda ya shigar da karar.

An yankewa Ali hukuncin ne karkashin sashi na 287 na Penal Code.

Da farko, dan sanda mai shigar da kara, Saja Godwin Ejeh ya shaidawa kotu cewar wani Ibrahim Haruna da ke zaune a Abacha Road ne ya shigar da karar a ofishin 'yan sanda da ke Maraba a ranar 24 ga watan Oktoba.

Ejeh ya ce wanda ya shigar da karar ya bayyana cewar a watan Yulin 2018 ne mai laifin ya shiga gidansa da ke addreshin Abacha Road kuma ya sace masa babur dinsa wanda kudinsa ya kai N150,000.

Dan sandan ya ce anyi kokarin ganin an gano inda babur din ta ke amma hakan bai yiwu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel