Dalilin da ya sa wasu manyan APC su ka shigar da Adams Oshiomhole Kotu

Dalilin da ya sa wasu manyan APC su ka shigar da Adams Oshiomhole Kotu

Wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC a Jihar Ondo sun maka Shugaban Jam’iyyar na kasa watau Adams Oshiomhole a gaban Kotu. ‘Ya ‘yan Jam’iyyar sun kuwa bayyana dalilin su na daukar wannan mataki.

Dalilin da ya sa wasu manyan APC su ka shigar da Adams Oshiomhole Kotu

An kai Oshiomhole da Hukumar zabe na kasa INEC Kotu a Ondo
Source: Depositphotos

Wasu ‘Yan Majalisa na Jam’iyyar APC da ke wakiltar Jihar Ondo a Majalisar Tarayya sun bayyana abin da ya sa su ka shiga Kotu da Adams Oshiomhole da kuma Hukumar zabe na kasa INEC bayan zabukan fitar da ‘Yan takara da aka yi.

Sama da mutum 100 ne dai su ke karar Shugaban Jam’iyyar na APC a Kotu inda Jagoran su Kenneth Olawale wani tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar yace sam Jam’yyar APC mai mulki ba ta gudanar da wani zabe a Jihar ba.

‘Yan takarar sun ce ba zabe aka yi wajen fitar da wadanda aka ba tikitin Jam’iyyar APC a zaben 2019 ba inda su ka bayyana cewa an ba ‘Yan daba makamai ne aka yi masu barazana aka hana su shiga zaben na fitar da gwanin da aka shirya.

KU KARANTA: An gano wasu ja’irai za su yi wa INEC kutse a lokacin zaben 2019

Wadanda su ka kai Oshiomhole da Jam’iyya da Hukumar zabe na INEC gaban Kotu sun hada da; Eni Omosule, Mukaila Ayorinde Ajakaye, Coker Malachi, Ayodeji Arowele, Dele Ologun, Olaposi Joe Babatunde da Agunloye Taiwo.

Lauyan da ke kare wadannan ‘Yan APC yana kukan cewa Jam’iyyar ta sabawa tsarin mulki da ka’idojin zabe da kuma dokokin kasa wajen fitar da ‘Yan takaran ta. A dalilin haka ne za a nemi Kotu tayi watsi da ‘Yan takarar APC a 2019.

‘Ya ‘Yan Jam’iyyar sun kuma nemi reshen Jam’iyyar APC na Jihar Ondo karkashin Ade Adetimehin da kuma Mai ba Jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a watau Babatunde Ogala su kare kan su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel