Da dumi-dumi: An cafke mutane 6 da suka kashe basaraken jihar Kaduna

Da dumi-dumi: An cafke mutane 6 da suka kashe basaraken jihar Kaduna

Jami'an tsaro sunyi nasarar kama wadanda su kayi garkuwa da sarkin masarautar Adara da ke karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna, Cif Maiwada Galadima (Agom Adara).

A yau Laraba ne aka gabatarwa manema labarai mutane shidan a hedkwatan hukumar yan sandan farin kaya (DSS) na jihar Kaduna.

A jawabin da ya yiwa manema labarai a yau, Direktan hukumar ya bayyana cewa an kamo wadanda ake zargin ne a wurare daban daban a Igabi, Soba Kachia da kuma garin Jos na jihar Plateau.

Da dumi-dumi: An cafke mutane 6 da suka kashe basaraken jihar Kaduna
Da dumi-dumi: An cafke mutane 6 da suka kashe basaraken jihar Kaduna
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya maka Sufeta Janar na 'yan sanda a kotu, ya nemi a biya shi N1bn

An dai sace sarkin ne tare da matarsa inda daga baya aka sako matarsa amma shi kuma aka tsinci gawarsa a jihar ta Kaduna.

Rasuwar sarkin ya janyo barkewar sabuwar rikici a jihar ta Kaduna wanda hakan yasa gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci kafin daga baya abubuwa suka lafa aka sassaunta dokar.

Gwamna El-Rufai na jihar ya yi alkwarin cewar za a gudanar da sahihiyar bincike kuma a gano dukkan wadanda ke da hannu cikin kashe-kashen domin a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel