Zan saye wani Kulob din kwallon kafa idan na gagara sayen Arsenal – Dangote

Zan saye wani Kulob din kwallon kafa idan na gagara sayen Arsenal – Dangote

- Aliko Dangote yace zuwa shekarar 2020 zai taya Kungiyar Arsenal

- Attajirin ya ce amma idan Kroenke ya ki saida kulob din zai hakura

- Dangote yace idan har abin ya faskara zai nemi wani kulob ya saya

Zan saye wani Kulob din kwallon kafa idan na gagara sayen Arsenal – Dangote
Alhaji Aliko Dangote yace zai nemi Kroenke ya saida masa Arsenal
Asali: Getty Images

Mun ji labari cewa Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa yana nan da shirin sa na taya Kungiyar kwallon kafa na Arsenal sai dai kuma yace idan hakan ya gagara zai hakura ya nemi wani kulob ya saya saboda yana son kwallon kafa.

Mai kudin na Afrika Aliko Dangote ya bayyanawa gidan Talabijin na Bloomberg cewa da zarar ya kammala gina matatar man fetur din sa da ke Legas zai karkatar da hankalin sa zuwa Kungiyar wasan kwallon kafan nan na Arsenal.

Aliko Dangote yana sa rai ya rika samun Dala Biliyan 30 kowace shekara a kamfanin da yake ginawa a Legas wanda zai rika tace danyen man fetur. Idan har mai kudin ya cika wannan buri na sa ne zai nemi Stan Kroenke ya saida masa Arsenal.

KU KARANTA: Mai kudin Afrika Dangote zai kashe Miliyoyin kudi a Katsina

Alhaji Aliko Dangote yana da burin ganin ya saye Arsenal tun ba yau ba don haka yake ganin zai jarraba sa’ar sa a kan Kroenke wanda yanzu kusan shi yake da mallakar Kulob din bayan ya saye kaf hannun jarin Attajirin nan Alisher Usmanov.

Dangote mai shekaru 61 a Duniya ya ba sama da Biliyan 11 baya kuma ya zage wajen neman bunkasa kamfanonin sa har a Turai. Attajirin yace lallai ko bai saye Arsenal ba, zai nemi wata Kungiyar kwallon kafa ya saya nan da shekarar 2020.

Tun kwanaki Aliko Dangote yace akwai wasu ayyuka da ya sa gaba wanda su ka hana sa sayen Kungiyar. A baya Dangote ya bayyana cewa da zarar ya sayen Kungiyar zai kori wasu manyan Kulob.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel