Dubu ta cika: Yansanda sun yi ram da wasu miyagun mutane 3 bayan sun tono wata gawa
Rundunar Yansandan jahar Nassarawa ta sanar da kama wasu mutane uku yan yankan kai a garin Lafia yayin da suke dauke da sabbin sassan jikin mutum na wata gawat da suka tono, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Kennedy Idrisu ne ya tabbatar da haka a ranar Talata 6 ga watan Nuwamba, inda yace dakarun Sojan kasa ne suka kama mutanen a ranar Juma’a, inda suka mikasu ga rundunar Yansanda.
KU KARANTA: Sarkin Gombe ya gina wani katafaren Asibiti don amfanin talakawansa
“Mutanen uku sun tafi wata makabarta dake Mararraban Akuza dake wajen garin Lafia a ranar 1 ga watan Nuwamba, inda suka hako gawar wani mutumi da ba’a dade da binneshi ba, suka guntule masa hannu, sa’annan suka sake binneshi.
“Sai dai da jama’an unguwar suka samu wannan labari, suka suka fito kwansu da kwarkwatansu suka yi cincirindo akan mutanen, inda suka fara lakada musu dan banzan duka, da kyar Sojojin suka kwaceshi, suka mikashi ga Yansanda.
“Ama ko kafin Sojojin su isa wurin, jama’a sun jikkata guda daga cikin mutane ukun, wanda a yanzu haka yana samun kulawa a asibitin kwararru na Dalhatu Araf dake garin Lafiya.” Inji Kaakakin Yansandan.
A jawabinnasa, Kennedy yace zasu gurfanar da miyagun mutanen kuma marasa Imani gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike akan lamarin don su gano niyyarsu.
Daga karshe kuma yayi kira ga jama’a dasu guji aikata miyagun laifuka, su rungumi zaman lafiya cikin amana da lumana, don kuwa a cewarsa rundunar Yansandan jahar ta shirya tsaf don yaki da duk wasu masu aikata miyagun laifuka a jahar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng